Wani babban jami’in hukumar abinci ta majalisar Dinkin Duniya yace kasashe dake Asiya suna fuskantar mummunar cutar dabbobi da ake kira Foot and Mouth Disease.Rabon da aga haka shekaru hamsin da suka wuce.
Jan Slingerbath,ya gayawa sashen Koriya na Muriyar Amurka cewa hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido sosai kan annobar a kasar Mongolia,da China, da Rasha. Haka kuma yace Koriya Ta Kudu da Japan suma cutar ta bulla cikin kasashen,haka kuma akwai damuwar cutar tana yaduwa a Koriya Ta Arewa.
Cutar tana kama dabbobi kamar Shanu,aladu,bareyi,da kuma tumaki.Jiya Jumma’a Slingerbath yace da alamun dangin bareyi masu shawagi tsakanin China da Mongolia suna daga cikin masu yada cutar.