Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer: Tarzomar Matasa Ta Janyo Takun Saka Tsakanin 'Yan Siyasa


A jamhuriyar Nijer wata sabuwar takaddama ta kunno kai bayan da wasu magoya bayan jam’iyyar PNDS mai mulki suka zargi jam’iyyar adawa ta Moden Lumana da hannu a zanga-zangar matasa da aka yi fama da ita a ‘yan kwanakin nan a birnin Yamai sakamakon kosawa da dokar hana fita da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Tun a farkon makon jiya ne matasa suka fara bijire wa dokar hana fita da hukumomi suka kafa daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe har suka yi ta kona tayoyi a manyan titunan birnin Yamai yayin da a wasu unguwannin mutane suka nuna kosawa da dokar hana sallar Juma’a, abinda wasu magoya bayan jam’iyya mai mulki ke kallo a matsayin wani sabon salo na ‘yan hamayya, a cewar Assoumana Mahamadou kakakin jam’iyar PNDS.

Da take maida martani akan wannan zargi uwar jam’iyyar adawa ta Moden Lumana ta nisantar da kanta daga zanga-zangar ta matasa.

Bana Ibrahim Kaza, kusa ne a wannan jam’iyya ya ce, wannan zargi ba gaskiya ba ne, tun da daga birnin Zindar aka fara zanga-zangar.

Tuni dai aka ce an hango wasu sanannun mutane suna mu’amulla da matasan da suka shirya wannan tarzoma.

Domin wanke kanta daga abinda ta kira kazafi, jam’iyyar Moden Lumana ta fara yunkurin shigar da kara a gaban kotu.

‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla a kokarinsu na murkushe wannan tarzoma, abinda ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali a unguwannin da aka yi artabu tsakanin jami’an tsaro da matasa. A sanarwar da sashen yada labarai a hukumar ‘yan sanda ya fitar, an bayyana cewa mutane 108 ne suka shiga hannu sanadin wannan zanga-zanga ta daren ranakun 17, 18 da 19 ga watan Afrilu yayin da a take aka tusa keyar 10 daga cikinsu zuwa gidan yarin Koutoukale.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


Saurari karin bayani cikin sauti.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG