Karin wasu mambobin babbar jam’iyyar adawa ta Sudan ta Kudu sun koma jam’iyya mai Mulki da shugaban kasa Salva Kiir ke jagoranta, inda ‘daya daga tsoffin mambobin ke zargin mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar da gudanar da jam’iyyar adawar tamkar kamfanin gidansu.
Dak Duop Bichiok, tsohon dan jam’iyyar SPLM-IO ya sanar da murabus dinsa tare da daruruwan magoya bayansa dake kasashen waje a wani taron manema labarai a Juba, a karshen makon da ya gabata.
Ya ce “Muna ayyana cewa yanzu bama tare da Dakta Riek Machar, kuma bamu kadai ba ne. Muna da kungiya a Nairobi da Masar da Khartoum, haka kuma a birnin Addis Ababa dama sauran kasashe a fadin duniya.”
Facebook Forum