Aiyukan raba katunan zabe ya kankama a jamhuriyar Nijar, sai dai ‘yan matsaloli da baza a rasa ba duk da kyakkaywan tsarin da akayi.
Malam Sadisu Abdu, dan kwamitin raba katunan zabe yace wasu mutane gabadaya suke tahowa da kuma yawan katunan zaben a wasu wurare yafi yawan masu jefa kuri’a dake kan kundin rajista, toh, nan ake samun ‘yan matsaloli.
Tashoshin zabe da dama ne aka kebe domin gudanar raba katunan zaben wasu daga cikin da wakilin muryar Amurka, ya ziyara wasu sun sami katunan wasu ko sun layi suna jira. Amma daga dukkan alamu yawanci jama’a sun gamsu da yadda alamarin ke tafiya.
Masu unguwani ma ba’a barsu a baya ba wajen hada kawunan talakawansu domin ganin cewa sun fito domin karbar katunan zabe wanda ke zaman makami a garesu.