Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kara Tsawo Hutun Zubar Dusar Kankarar Da Ta Mamaye Birane


Wani Titin Birnin Washington Da Aka Fara Sharewa
Wani Titin Birnin Washington Da Aka Fara Sharewa

Gwamnatin kasar Amurka ta bada hutu jiya Litinin da ma yau Talata ga daukacin ma'aikatan gwamnati dake cikin Washington ta gundumar Colombia domin jama'a su samu damar gyara muhallansu da kankara ta mamaye.

Suma yaran makaranta ba a barsu a baya ba domin kuwa daukacin makarantu duk sun kasance a kulle suna hutun zubar dusar kankarar da aka dade ba a ga irinta a kasar ba.

Duk da kokarin da gwamnati tayi na ganin ta share manya-manyan tituna a ciki gundumar ta Colombia da jihar Maryland har, yanzu akwai wasu titunan da dusar kankaran take jibge kamar ba a dibarta.

Wanda hakan kuma ya haifar da cunkoson motoci a wasu sassan biranen. Jiragen sama da suka kai 1500 ne aka hana tashi da sauka a tashoshin jiragen saman garuruwan da suka hada Washington da Baitimore da New York da kuma Philadelhia duk a jiya Littinin.

Yayin da jiragen kasa suka fara aiki a hankali kuma kyauta aka shiga. Wannan dusar kankarar dai tasa mutane da yawan gaske a birnin New York kauracewa birnin zuwa kudancin jihar.

Inda kankarar ta fi zuba matukar gaske sune garuruwan na Baltimore da da kuma Washington. Yanzu dai abubuwa sun fara komawa dai-dai, duk da yake ana ganin tari-tarin dusar kankarar a sassa da dama na wuraren da ta yiwa dirar mikiya.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG