‘Yan harin kunar-bakin-wake sun kai hare-hare kan wani gari a yankin kuryar arewacin kasar Kamaru, inda ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram suka saba kai hare-hare.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci wani jami’in yankin yana fadin cewa ‘yan kunar bakin wake su 4 sun kai farmaki yau litinin da asuba kan garin Bodo suka kashe mutane akalla 25. Jami’in yace ‘yan kunar bakin wake biyu sun kai farmaki kan babbar kasuwar garin, yayin da sauran suka tayar da bama-baman jikinsu a manyan kofofin shiga da fita daga cikin wannan gari na Bodo.
Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren, amma ana kyautata zaton kungiyar nan ce ta Boko Haram.
Kungiyar ta fara kai munanan hare-hare cikin Kamaru a shekarar 2013 a lokacin da gwamnatin kasar ta fara daukar matakan murkushe tsagera masu amfani da yankin a zaman sansanin kaddamar da hare-hare a cikin Najeriya.
Garin Bodo yana bakin iyakar Kamaru da Najeriya. A watan da ya shige wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun tayar da bama-bamai suka kashe kawunansu su kadai.
Kamaru tana cikin kasashe biyar da suka hadu suka kafa rundunar hadin guiwa domin yakar Boko Haram.