Bayan da kotun daukaka kara tayi watsi da batun ba Hama Ahmadou beli wasu magoya bayansa sun yi dafifi a harabar kotun suna kuka tare da zargin gwamnatin kasar da kulla wata makarkashiya ga dan takararsu.
Mutane sun nuna fushinsu dangane da hukuncin kotun. Wata cikin hawaye tace tana bayan Hama kodayaushe kuma komi aka yi ba zata bar binsa ba.
Shugaban wata kungiya dake goyon bayan Hama Ahmadou, Ibrahim Bana ya nuna rashin jin dadi akan hukuncin kotun. Yace a ganinsu shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou yana tsoron Hama Ahmadu saboda haka zai yi duk iyakacin kokarinsa ya hanashi takara.
Saidai a martanin da ta mayar jam'iyyar PNDS Tarayya dake mulkin kasar ta bakin kakakinta Alhaji Asumana Muhammadou yace ko kadan babu hannun gwamnati a lamarin da Hama Ahmadou ke ciki.Yace kotu ce dake yi da Hama saboda ya taka doka.
Hama Ahmadou na cikin mutane fiye da ashirin da gwamnatin kasar ke zargi da sayen jarirai daga Najeriya saidai ya zuwa yanzu shi kadai ya rage a gidan yarin da aka ajiyeshi tun ranar 14 ga watan Nuwambar 2015 jim kadan bayan da ya dawo daga gudun hijirar watanni goma sha biyar a kasar Faransa.
A wani bangare kuma daukacin lauyoyin Nijar sun shiga yajin aikin wuni daya yau Litinin domin nuna bacin rai a kan matakin hanasu ganawa da wasu 'yan adawa da hukumomin Nijar suka kulle ba tare da sanarda danginsu laifin da ake zarginsu da aikatawa ba.
Ga karin bayani.