Za'a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki ranar 21 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Masu kula da alamuran dake faruwa na ganin fitowar 'yan takara masu tarin yawa wata alama ce na cigaban dimokradiya da kasar ta samu tunda aka fara mulkin farar hula kimanin shekaru 21 da suka wuce.
Wani Dambaji dan gwagwarmaya a karkashin wata kungiya yace idanun 'yan Nijar sun bude akan harkokin siyasa. Yace ko mutanen daji sun fahimta, sun gane menene dimokradiya.
Shigar matasa cikin siyasar kasar ta sa mutane na tofa albarkacin bakinsu. Masaud Ibrahim yace sakamako ne na rarrabuwar kawunan wasu manyan jam'iyyun siyasa da suka fuskanta cikin shekarun baya bayan nan.
Rashin samun mace ko daya cikin 'yan takara goma sha shida nada nasaba da rashin kudi da mata ke fama dashi. Matsalar Boko Haram ta hana mata shiga daji nman kuri'u.
Kotu zata tantance 'yan takaran ranar tara ga wannan watan.
Ga karin bayani.