Ziyarar wacce ke cikin sababbin jerin ayyukan da majalisar dokokin kasa ta kudirtawa kanta a baya bayan nan, ta kasance wata damar tuntubar rukunonin al’ummar Diffa domin tantance zahirin dalilan da ke maida hannun agogo baya a yakin da dakarun Nijar ke kwafsawa da kungiyar Boko Haram yau shekaru sama da 4.
A karshen wannan rangadin tawakar karkashin jagorancin Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasa Hon. Hama Assa, ta gano abubuwa da dama ta kuma gargadi al’umma akan wasu mahimman batutuwa.
Sai dai a yayin wannan ganawa wani mai magana da yawun al’ummar yankin Diffa ya gabatar da wani sakon da suke bukatar a isar da shi zuwa ga shugaban kasa Mahamadou Issouhou.
A nan gaba kadan majalisar dokokin kasa za ta gudanar da mahawarar bainar jama’a akan abubuwan da rahoton tawwagar kwamitin tsaron ya gano a yayin wannan ziyara da nufin tantance shawarwarin da zasu taimakawa gwamnati wajen shayo kan matsalar tsaron da ke ci gaba da lakume rayukan al’umma tare da haddasa asarar dimbin dukiyoyi da kaurar jama’a.
Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma
Facebook Forum