Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar zagayen yankunan kasar, da nufin jan hankulan jama’a akan bukatar baiwa jami’an tsaro hadin kai, a yakin da suke karawa da ‘yan ta’adda. Bayan la’akari da babbar barazanar da ake fuskanta daga kungiyoyin ta’addanci irinsu Boko Haram wace aka gano cewa tana bullo da sababbin salon hare-hare a yankin Diffa.
Da yake jawabi a yayin bukin bude taron shekara shekara ne shugaban majalisar dokokin jamhuriyar Nijar Ousseini Tinni ya sanarda shirin aikewa da tawagogi zuwa illahirin jihohin kasar, don fadakar da al’uma bukatar samun hadin kansu a yakin da dakarun gwamnati ke fafatawa da ‘yan ta’adda.
Sabon salon da kungiyar Boko Haram ta bullo da shi a ‘yan watannin nan a yankin Diffa wani abu ne dake bukatar tsaurara matakai, don dakile dukkan wani yunkurin bazuwar wannan matsala zuwa wasu yankunan na daban.
Dan majalisar Dokoki Lamido Moumouni Harouna na daga cikin wakilan al’umar yankin Diffa a majalisar dokokin Nijar, yace a shirye suke su tunkari matsalar kai tsaye.
Lura da yadda matsalar tsaro ke mayarda hannun agogo baya a dukkan wasu ayyukan da suka shafi ci gaban al’uma ya sa ‘yan majalisar, shan alawashin fitar da talakawa daga kangi, kamar yadda dan majalisar dokokin kasa Sama'ila Hatimou Mai Aya ke bayyanawa.
Satar mutane domin neman kudin fansa da kisan fararen hula, da jami’an tsaro ko cinnawa gidajen jama’a wuta hade da kai harin kunar bakin wake, na daga cikin hanyoyin da Boko Haram ke amfani a wannan yaki da ya tilasatawa dubban jama’a tserewa daga matsugunansu, duk kuwa da irin matakan da gwamnatin Nijar ke dauka, hakan yasa ake ganin bukatar samun hadin kan talakawa don kawo karshen matsalar.
Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Facebook Forum