Kungiyar kwararun likitoci a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci hukumomin kasar su gaggauta daukan matakai don magance wasu matsalolin da su ka addabi magoya bayanta, a lokacin da su ke gudanar da aiki, ciki kuwa har da barazana da rayuwar da jami’an kiwon lafiya ke fuskanta a wasu yankunan kasar.
Matsalar tsaron da ake fama da ita a yankunan Diffa da Tilaberi na daga cikin batutuwan da kungiyar Symphamed ta bayyana damuwa akansu, a cikin wata sanarwar da ta fitar bisa la’akari da yadda lamarin ke haddasawa likitoci cikas a lokacin da su ke gudanar da aikinsu.
Dr Habou Abdourhaman, shine sakataren tsare tsare na wannan kungiyar ya ce, an hana yawo da motoci da daddare, saboda an kafa dokar ta baci, inda likitocin basa iya fita da daddare domin zuwa gurin aiki, da kuma irin barazanar da su ke fuskanta daga gurin bata gari.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma :
Facebook Forum