Suna zargin ya yi amfani da wadannan kaddarorin ne a yayin zagayen siyasar da ya gudanar a baya bayan nan a wasu jihohin kasar sai dai a bangaren masu mulki ana kallon wannan korafi tamkar irin na wanda ya fara ganin alamun shan kaye a zabe.
Sanin irin rawar da ministan cikin gida ke takawa wajen shirya zabe, da gudanar da shi anan Nijar, ya sa shugabannin jam’iyun adawar kasar fara korafi game da zagayen da dan takarar jam’iyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed ya fara gudanarwa a sassan kasa.
Dalilin da ya sa suka soma yunkurin shigar da kara a gaban kotu domin ta hukunta ministan cikin gidan dai dai da abinda kundin zabe ya yi tanadi, kamar yadda suka bayyana a sanarwa, da Malam Rabiou Gonda ya fassara.
Domin kawar da dukkan wani tunani mai nasaba da dalilan bangarancin siyasa, kawancen na FRDDR ya kaddamar da rajistar sunayen ‘yan kasa dake fatan ganin an gurfanar da shugaban jam’iyar ta PNDS a gaban kotu.
Da yake maida martani akan wannan batu sakataren kula da harakokin zabe a jam’iyar PNDS TARAYYA Alhaji Boubacar Sabo, yace ba su da fargaba game da wannan yunkuri.
‘yan adawar sun kudiri aniyar gudanar da zanga zanga a ranar 7 ga watan Satumba mai shirin kamawa, da nufin takawa gwamnatin Nijar burki wace suke zargi da yin kaka gida a al’amuran tsare tsaren zabe, abinda suke ganin idan ba a kula ba, demokradiya za ta fuskanci mummunan koma baya a wannan kasa.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum