Wata majiya mai tushe a Nijar, ta shaidawa Sashen Hausa na Muriyar Amurka cewa, an kama babban hafsa a rundunar sojin kasar wanda yake da mukami mafi girma na biyu bayan shugaban kasar,bisa zargin kitsa juyin mulkin soja.
A safiyar jiya laraba ce aka Kama Kanal Abdullahi Badie,wanda kamin haka,shine sakatare na din din a majalisar koli ta mulkin sojan kasar. Ranar lahadi ce fadar gwamnatin Nijar ta bada sanarwar soke wan nan mukami na sakataren majalisar kolin. Bata kuma bada Karin bayani kan dalilin daukan wan nan mataki ba.
Banda kanal Badie, an kuma kama wasu hafsoshi biyu.Sune Kanal Diallo Ahmadu, kwamishinan gwamnati a kotun hukunta sojoji,da kuma Leftanar kanar Abdullahi Siddique Isa,babban kwamndan dogarawan fadar shugaban kasa,wanda tuni aka nada mataimakinsa ya karbi wan nan mukami.
Duk da cewa babu karin bayani da suka bayar,an juma ana yada jita jitar an sami rarrabuar kawuna tsakanin shugabannin mulkin sojin kasar.A gefe guda,wasu hafsoshi sun bayyana bukatar kara wa’adin gwamntin wucin gadin kasar,amma shugaban kasa, Janar Salihu Jibo,ya dage tilas a mika mulki kan wa’adi da aka tsayar.
A karshen wan nan watan ne ake sa ran yin zaben raba gardama kan sabon tsarin mulkin Nijar. Za’a yi zabe cikin watan Janairu,a mika mulki cikin watan Afrilun badi.