Nijar tana karyata rahoannin dake cewa an kama mukaddashin shugaban mulkin sojin kasar. Shugaban mulkin sojan kasar Janar Salou Djibo,ya gayawa wata tawagar kungiyar ECOWAS cewa ba’a kama kowa ba,kuma shirin mika mulkin kasar zai ci gaba kamar yadda aka shirya.
Tun da farko na’ibin shugaban Kanal Abdoulaye Badie ya gayawa Muriyar Amurka daga gidansa dake babban birnin kasar Niamey,inda ya karyata rahotannin cewa an kama shi.
An fara yada laabrin kamunsa ne kwanakin bayan da shugaban kasar ya sanya hanu kan dokar da ta soke mukaminsa na sakataren din din na majalisar mulkin sojin kasar.
Badie ya gayawa Muriyar Amurka cewa har yanzu ba’a gaya masa dalilin korarsa daga aiki ba.
Ahalin yanzu kuma,jakadun yankin sun bayyana cewa Nijar ta damu kan ci gaba da kasancewar sojojin Faransa cikin kasar.
Zaman dar dar na ta karuwa tun loakcinda Faransa ta tura sojoji 80 zuwa kasar, domin taimakawa wajen neman ma’aikatan kamfanonin Faransa biyu da wata kungiya mai alaka da al-Qaida take garkuwa das u.