Wata tawagar Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta isa Sudan domin tattaunawa a kan kuri’ar raba-gardamar da zata tantance ko yankin kudancin Sudan zai zamo kasa mai ‘yanci.
Daruruwan ‘yan Sudan dake jinjinawa sun yi layi a kan titunan Juba, babban birnin kudancin Sudan domin yin marhabin da tawagar jiya laraba. Wakilan na Kwamitin Sulhu sun gana da shugaban kudancin Sudan, Salva Kiir da wasu jami’an yankin.
Babban gurin wannan tawaga shine hana abkuwar duk wani jinkiri ga kuri’ar raba-gardamar ta ranar 9 ga watan Janairu, wadda aka yi alkawarin gudanarwa a yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005 wadda ta kawo karshen yakin basasar arewaci da kudancin Sudan. ‘Yan kallo sun ce ana jan kafa wajen shirye-shiryen gudanar da zaben, kuma jinkirta shi na iya haddasa barkewar sabon fada.
Tankiya tana karuwa a tsakanin arewaci da kudancin Sudan a yayin da wannan kuri’a take kusantowa. Har ila yau, sassan su na da sabanin ra’ayi a kan wata kuri’ar dabam ta raba-gardama wadda ita ma za a gudanar a ranar 9 ga watan Janairu a kan makomar yankin Abyei mai arzikin man fetur. Masu jefa kuri’a na Abyei zasu yanke shawara a kan ko wane bangaren Sudan suke son shiga. Sai dai arewaci da kuma kudanci sun kasa daidaitawa a kan bakin iyakar yankin. Haka kuma ba su daidaita ba a kan ko za a kyale kabilar Misseriya mai alaka da arewaci ta jefa kuri’a.