Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Na Daf Da Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Aikata Almundahana


NETANYAHU
NETANYAHU

Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na daf da gurfana a gaban kotu a gobe Talata a karon farko a shari’ar da yake fuskanta ta zarge-zargen aikata almundahana, inda ya musanta aikata ba daidai ba

Wannan wata muhimmiyar ci gaba ce a shari’ar dake zuwa a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar yaki a Gaza tare da sammaci daga kotun duniya akan tuhume-tuhumen aikata laifuffukan yaki.

COURT
COURT

A cikin kasarsa kuma, Netanyahu na fuskantar shari’a akan zarge-zargen zamba da cin amana da karbar rashawa a wasu al’amura 3. Netanyahu ya musanta zargin aikata ba dai dai ba, sai dai gurfanarsa a gaban kotu tawaye ce a tsawon shekarun daya shafe yana siyasa, wacce ta saba da kimar kasaitaccen shugaba mai mutunci da yake kokarin nunawa.

Magoya bayan Hezbollah da Falasdinawan Gaza
Magoya bayan Hezbollah da Falasdinawan Gaza

Shari’ar za ta cinye wani gwaggwaban kaso na lokacin Netanyahu a wannan lokaci mai matukar mahimmanci ga Isra’ila. Yayin da zai shafe makonni yana fuskantar shari’a, za’a bukace shi ya ci gaba da tasrifin al’amura a yakin Gaza da kula da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsa da kungiyar mayakan Hezbullahi ta Lebanon da kuma sa idanu akan barazanar dake fitowa daga kasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Iran.

Gaza
Gaza

Wannan ne zai zama karon farko da wani Firai Ministan Isra’ila zai gurfana a gaban kotu a bisa tuhumar aikata laifi, kuma sau da dama Netanyahu ya yi ta janyo tsaiko a shari’ar, yana fakewa da yakin Gaza da matsalolin tsaro.

Alkalan kotun sun bada umarnin a cigaba da shari’ar a gobe Talata, inda suka mayar da sauraron karar zuwa wata kotun karkashin kasa dake birnin Tel Aviv a matsayin matakin tsaro.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG