Al’ummar garin Lafia a jihar Nasarawa na ci gaba da gargadin junansu kan matakan da zasu bi wajen kaucewa ci gaba da rasa rayuka, bayan ambaliyar ruwa yayi sanadin rasa rayukan mutane uku a cikin ‘yan kwankin nan.
A hirar su da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, ta yi da Jibrin Zakari wanda ya ga lokacin da ruwan ya hallaka mutanen, ya bayyana cewa, kamata yayi jama’a su dauki matakan kare kansu. Ya kara cewa ya kamata, masu gidaje kusa da ruwa, su tashi, su koma wajen da babu irin wannan matsalar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Nasarawa, Zakari Zamani Alumaga, yace bayan wayar wa mutane kai, kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihar, gwamnati ta shirya sayen kayayyakin ceto na zamani don bada agaji wa wadanda suka shiga bala’i cikin gaggawa.
A saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Facebook Forum