Nasarar Donald Trump ta zo ne a daidai lokacin da kasashe ke hada kai domin yaki da ta'adanci musamman kasashen yankin tafkin Chadi a karkashin jagorancin Najeriya.
Ga mai sharhi akan alamuran yau da kullum Abubakar Ali na ganin nasar da Donald Trump ya samu a zaben Amurka zata zama tamkar allura ga kasashen Afirka ko Najeriya su dage wajen rage dogaro ga mutum domin nasarar cimma burin raya kasa da kuma diflomasiya.
Yace cin zaben Trump da irin maganganun da ya keyi musamman akan 'yan Najeriya zai zaburar da 'yan Najeriya din ne ba wai su dinga dogaro ga kasashen waje ba, suna sauraron wanene ya ci zabe wanene ya fadi.
Yadda Amurka ta dogara ga kasarta kuma kasarta kawai ta sani haka ma ya kamata 'yan Najeriya su dogara ga kasarsu. Ya kamata 'yan Najeriya su dogara ga kayan abincinsu da tufafinsu amma ba a dogara da wata kasar waje ba.
Masanin harkokin siyasa na Jami'ar Abuja Adulrahaman Abu Hamisu na ganin Trump na cika baki ne kawai domin neman kuri'un jama'a. Yayi maganganun da suke son su ji shi yasa suka soshi. Trump ya gane talauci ya yiwa wasu amurkawa katutu dalili ke nan yace zai kori baki domin ya ba 'yan gida ayyukansu. Za'a ga yadda zai kori mutanen.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.