Jamhuriyar kwango, ta sanya hanu kan wata yarjejeniya da ake gani zata shiga tarihi, ta dala milyan dari biyu, da zummar hana rusa makeken dazukan kasar, wanda shine na biyu a girma, baya ga dazukan da ake kira Amazon, da galibi suke kasashen da suke yankin Latin Amurka, su tara.
Kwango itace kasa ta farko da zata sanya hanu kan jarjeniyar, kan shirin da aka bullo da shi watanni bakwai da suka wuce, da zummar kare daji dake gabar ruwayen a yankin.
A bara ne aka kaddamar da shirin karkashin wasu kasashen Afirka biyar, tare da tallafi daga wasu kasashen turai. Shirin yana bukatar kasashe da suka amince da shirin, su zuba jari domin ganowa, su kuma yaki matakai da suke janyo sare dazukan.
Dajin dake yankin na kwango, girmansa ya kai kimanin murabba'in kilomita milyan biyu,kamar dai girman kasar Mexico. Amma dajin yana fuskantar koma baya, na kilomita dubu biyar da dari shida duk shekara, saboda noman manja.
Wata kungiyar da take rajin kare muhalli mai suna Global Witness da turanci, tana zargin manyan kamfanonin sarrafa katako a kasar, da ci gaba da keta dokokin kasar, da aka kafa da zummar kare dazukanta.
Shugaba Joseph Kabila, yayi alkawarin aiwatar da sauye sauye a fannin noma a kasar, wacce Allah ya yiwa albarkatun kasa dana noman.