A cewar wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar, an dau matakin ne a dukan kananan hukumomi 23 domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga bata gari dake bi suna fasa ma’ajiyar dukiyar al’umma suna kwashewa.
A halin yanzu dokar ta hana fita da shiga, wanda ta fara aiki nan take zata kasance na sa’oi 24 ne a dukkan fadin jihar har na wani locaci da gwamnati taga ya dace a sassauta.
Wannan na zuwa ne yayinda zanga zangar lumana na neman wasu sauye sauye da suka hada da sauke bangaren ‘yan Sanda na SARS ya rikide ya zama tashi hankali da bata gari suka shiga wawure dukiyoyin al’umma a wasu sassan kasar ke dada zama barazana ga harkar tsaro.
Jihar ta Kaduna dama ta dade tana fuskantar tashe tashen hankula dake jefa al’umma cikin zaman dar dar, dauk da cewa mahukunta da shugabannin addinai da na al’umma da jami’an tsaro na ta tattauna yadda za’a magance wannan matsalar.
Facebook Forum