Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAKASA BA KASAWA BA: Hira Da Wani Mai Larurar Tawaya Da Ke Sana’ar Kanikanci A Jihar Enugu, Yuni 22, 2023


Souley Mummuni Barma
Souley Mummuni Barma

Shirin Nakasa Ba Kasawa Ba na wannan makon ya sami bakuncin wani dan asalin jihar Adamawa da ke zaune a jihar Enugu a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Bakon shirin wanda ya tsinci kansa cikin halin tawaya bayan da ya yi fama da rashin lafiya a lokacin yarinta, bakanike ne da ya yi fice a garin Enugu wajen gyaran keke NAPEP da aka fi sani da adaidaita sahu.

Sa'idu Ali Mai Gyaran Keke NAPEP
Sa'idu Ali Mai Gyaran Keke NAPEP

Malan Sa’idu Ali, na alfahari da baiwar da Allah ya yi masa, dalili kenan ya rungumi sana’arsa a matsayin madogarar rayuwa.

A hirarsa da wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe, Malam Sa’idu ya fara da yin bayani game da ainahin yadda aka yi ya shiga halin Nakasa.

Sa'idu Ali Mai Gyaran Keke NAPEP
Sa'idu Ali Mai Gyaran Keke NAPEP

Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:

NAKASA BA KASAWA BA: Hira Da Wani Mai Larurar Tawaya Da Ke Sana’ar Kanikanci, Yuni 22, 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00

XS
SM
MD
LG