Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Taraba Ta Tallafawa Al’ummar Da Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Barna


Lamidon Kuma Alhaji Adamu Gambo Nimeso yana karban kayan abincin da aka kawo
Lamidon Kuma Alhaji Adamu Gambo Nimeso yana karban kayan abincin da aka kawo

Bayan ambaliyar ruwa da ta auku a wasu yankunan yankin Mambilla dake jihar Taraba arewa maso gabashin Nigeria, gwamnatin jihar ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa.

Dukiya na miliyoyin naira ne suka salwanta musamman amfanin gona a wasu yankuna na Mambillan, sanadiyar ambaliyar ruwa, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da na Yurum,Mbaso, Yana da Njeke dake cikin karamar hukumar Sardauna inda aka kai musu wannan tallafi na abinci da suka hada da buhunan masara dari biyu.

Alh, Abubakar Zubairu Kabri, hadimin gwamnan jihar, shine ya wakilci gwamnan jihar wajen bada buhunan hatsin.

Mai martaba Lamidon Kuma Alhaji Adamu Gambo Nimeso da shugaban karamar hukumar Sardauna Reverend Goodwill Sol sun nuna farin cikinsu da wannan tallafin da gwamnatin jihar ta turo.

Matsalar ambaliyar ruwa na neman zama ruwan dare a Najeriya, wanda kuma alkalumman hukumomin bada agaji a kasar ke cewa fiye da mutum dari sun mutu ta sanadiyar ambaliyar baya ga hasarar dukiya. Wannan al’amari ya faru ne yayin da aka soma sako ruwa daga madatsar ruwan Lagdo na kasar Kamaru dake makwabtaka da jihohin Taraba da Adamawa.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG