Gwamnatin Najeriya ta yi tayin bada tukuici domin samun bayanai kan mutumin da ake zargi da kitsa kai kazamin harin bom kan shelkwatar Majalisar Dinkin duniya a Abuja da yayi sanadin asarar rayuka.
Hukumar ‘yan sandan ciki sun bayyana jiya Lahadi cewa zata biya tukuicin naira miliyan 25 ga wanda zai samar da bayanan da zasu kai ga kama Mamman Nur.
Cibiyar tace Nur yana cikin kungiyar Islaman nan mai tatstsauran ra’ayi Boko Haram wadda ta dauki alhakin kai harin. Bisa ga cewar cibiyar Mamman Nur ya shirya kai harin ne bayan dawowarshi daga Somalia.
Harin da aka kai kan ginin Majalisar Dinkin Duniyan ya yi sanadin mutuwar mutane 23 da dama kuma suka jikkata.
An gurfanar da hudu daga cikin wadanda ake zargi da hada baki wajen kai harin a gaban kotu dake birnin tarayya Abuja ranar Jumma’a. Alkali ya bada umarnin ci gaba da tsare mutanen har zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba da zasu sake bayyana gaban kotun