Lauyoyin gwamnatin Nigeria sun zargi wasu mutane hudu da laifin shirya harin kunar bakin wake da aka kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria a watan jiya.
Jiya juma’a lauyoyi suka fadawa wata kotun majistire a Abuja cewa, Salisu Mohammed da Yunusa Muka’illa da Danazumi Haruna da kuma Abdulsalami Adamu yan kungiyar boko haram ne, kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin na ofishin Majalisar Dinkin Duniya.
Lauyoyin sun baiyana cewa mutane hudun, sune suka hada baki suka tura mai harin kunar bakin wake zuwa ginin. Su dai mutane hudun, wadanda basu amsa ko musunta zargin da ake yi musu ba, sun ce ya kamata a kai wannan batu nasu gaban wata babar kotu.
Alkalin kotu ya bada umarnin a ci gaba da tsare mutane har zuwa ranar uku ga watan nuwamban idan Allah ya kaimu. Jiya juma’a lauyoyi suka ce mutane ashirin da biyar ne suka mutu a hatrin da aka kai a watan Augusta.