Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Zaben Shugaban Kasa Yau Asabar


Fasta na shugaba Goodluck Jonathan a Jos, Jihar Filato, Jumma'a 15 Afrilu, 2011
Fasta na shugaba Goodluck Jonathan a Jos, Jihar Filato, Jumma'a 15 Afrilu, 2011

Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP yana fuskantar kalubale sosai a zaben na yau asabar, musamman daga dan takarar jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya

‘Yan Najeriya su na shirin zaben shugaban kasa yau asabar, a zaben da akasarin masana ke fadin cewa shugaban dake kan mulki, Goodluck Jonathan, shi ne zai lashe cikin sauki.

Wakiliyar Muryar Amurka Julia Ritchey ta ce hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce ta shirya tsaf ma zaben shugaban kasar, a bayan da aka samu cikas a zaben farko da aka gudanar na ‘yan majalisun dokokin tarayya.

Duk da cewa ana hasashen shugaba Jonathan zai lashe wannan zabe, yana fuskantar kalubale sosai daga tsohon shugaban soja Janar Muhammadu Buhari mai ritaya mai shekaru 68 da haihuwa da kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Nuhu Ribadu mai shekaru 50 da haihuwa.

Wani mai jefa kuri’a mai suna Mario Samuel yace shi kam ya yanke shawarar wanda zai jefawa kuri’arsa, yana mai cewa, "Janar Buhari zan zaba a saboda shi kadai muka yarda da shi a kan sauran dukkan ‘yan takarar." Samuel yace bai yarda cewa jam’iyyar PDP ta shugaba Jonathan zata iya takalar matsalar handama da babakeren da suka zamo ruwan dare ba.

Wani mai jefa kuri’ar wanda ya gama karatun jami’a amma ba ya da aikin yi, yace a da har yayi niyyar zai zabi Buhari, amma sai ya sauya tunaninsa a bayan da shugaba Jonathan yayi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasan kasar. Ya ce shi kam ma Goodluck Jonathan zai jefa kuri'arsa.

Jam’iyyar PDP dai ta lashe dukkan zabubbukan shugaban kasar da aka yi a Najeriya tun lokacin da sojoji suka maida ma fararen hula mulki a 1999. Amma a zaben ‘yan majalisar dokokin da ya shige, jam’iyyar ta yi hasarar kujeru da yawa a yankunan arewaci da kuma kudu maso yammacin kasar.

XS
SM
MD
LG