Rahotannin da aka samu ya zuwa yanzu sun nuna cewa an gudanar da zaben shugaban kasar Nijeriya cikin kwanciyar hankali, sabanin akasarin zabubbukan baya da tashe-tashen hankula da magudi su ka dabaibaye su.
Masa lura da yadda al’amarin ke gudana sun ce an fito sosai a jiya Asabar au don zaben shugaban kasa mai ci Goodluck Jonathan don fara cikakken wa’adinsa na farko au a zabe daya daga cikin manyan masu kalubalantarsa biyu. Mr Jonathan ya dare gadon mulki bara ne bayan rasuwar mutumin da ya gada, Shugaba Umaru Musa Yar’adua.
An dau tsauraran matakan tsaro a fadin wannan kasar ta yammacin Afirka, wadda it ace kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka. Kuma duk da fashe fashen wasu abubuwa biyu a birnin Maiduguri na Arewacin Nijeriya da safiyar jiya Asabar, masu lura da yadda abubuwa ke gudana sun ce an cigaba da kada kuru’u cikin kwanciyar hankali in ban ‘yan cuwa cuwa nan da can.
Har an fara kidaya kuri’u a wasu mazabun ya zuwa yammacin jiya Asabar.
Mr. Jonathan ya gaya wa masu kada kuri’a cewa kasarsa na gab da shiga sabuwar marra a siyasance a daidai lokacin day a ke kada kuri’arsa. Ya yi alkawarin za a gudanar da zaben cikin adalci kuma ya ce ba zai murde sakamakon ba.
Ga dukkan alamu yana gaba-gaba a takarar kuma ya yi alkawarin farfado da tattalin arziki, da kiwon lafiya da ilimi a wannan kasa mai arzikin man fetur.
Yana fuskantar kalubale mai tsanani daga ‘yan takara biyu da su ka kasa yin taron dangin da zai kai ga zabe zagaye na biyu.
Babban mai kalubalantar Jonatahn shi ne tsohon shugaban mulkin soji Muhammadu Buhari, wanda ya taba shiga takara har sau biyu bai yi nasara ba. A lokacin da Buhari ke kada kuri’arsa jiya Asabar y ace shi ba zai kalubalanci sakamakon wannan zaben ba idan ya fadi.
Shi ma tsohon shugaban hukumar yaki da almundahana da dukiyar jama’a Nuhu Rubadu, ana ganin yana iya shiga karawa ta zagaye na biyu.