‘Yan Najeriya suna zaben shugaban kasa,inda ake sa ran shugaban kasa Goodluck Jonathan zai sami nasara a kudurinsa na ci gaba da jagoran kasar mafi yawan al’uma a Afirka.
An tsananta matakan tsaro a mazabu,yayinda aka sami labarin wasu abu sun fashe a birnin Maiduguri a safiyar Asabar din nan, haka ya kara tada hankula,sai dai ba’a bada rahoto nan take kan yawan mutane da suka jikkata,da kuma tasirin haka kan zabe da ake yi.
Shugaba Jonathan yana fuskantar kalubale daga ‘yan hamayya da suka kasa yin kawance domin hana a yi zaben fidda gwani.
Manyan ‘yan hamayya biyu da suke kalubale ga Jonathan sune tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari,da kuma Nuhu Ribadu,tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaba Jonathan yayi alkawarin inganta tattalin arziki,kiwon lafiya,ilmi,a kasar mai arzikin mai.
Shi shugaba Muhammadu Buhari yayi alwashin kauda cin hanci da rashawa da samarda abubuwan more rayuwa,yayinda Nuhu Ribadu yace babban abinda zai mai da hankali akai shi yaki da talauci.
Hukumomin sun bada labarin rufe kan iyakokin kasar,kuma an baza jami’an tsaro ta ko ina cikin kasar domin kauda tashe tashen hankula.