Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Kasa A Legas Ya Kai Shida


Yadda jirgin kasa ya yi karo da bas a Legas
Yadda jirgin kasa ya yi karo da bas a Legas

Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga Abeokuta yana kan hanyarsa ta shiga Legas a lokacin da hatsarin ya auku.

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin kasa ya yi karo da wata motar bas a Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ya kai shida.

Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis yayin da bas din wacce ke dauke da ma’aikatan gwamnati ke kokarin ketara hanyar layin dogo a yankin Ikeja da ke birnin na Legas.

Da farko, rahotanni sun ce ruwaito mutuwar mutum uku.

Bayanai sun yi nuni da cewa mutum 84 sun ji raunuka daban-daban, an kuma garzaya da su asibiti bayan aukuwar hatsarin.

Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga Abeokuta yana kan hanyarsa ta shiga Legas a lokacin da hatsarin ya auku.

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA a Legas, Ibrahim Farinloye wanda ya tabbatar da aukuwar hatsarin, ya fadawa gidan talbijin na Channels cewa akwai mata biyu daga cikin wadanda suka mutu.

Hukumar jiragen kasa ta Najerita ta ce ta fara binciken musabbabin wannan hatsari.

Shi ma a bangaren sa Ministan Sufurin Jiragen Sama had Sirika yace wata hukumar binciken ababen hawa zata gidanr da bincike akan wannan hatsari.

Hatsarin jirgin kasa da mota a Najeriya ba bakon abu ba ne.

Ko a karshen shekarar da ta gabata, wani jirgin kasa ya yi awon gaba da motar wata matashiya a birnin Abuja yayin da take kokarin ketara hanyar layin dogon, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.

XS
SM
MD
LG