Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce ta yi nasarar samun alluran rigakafin cutar sankarau ga kananan yara.
Bayanai na nuni da cewa kimanin mutane fiye 10,000 ne ke kamuwa da cutar sankaura a Najeriya a kowacce shekara, inda fiye da 1,000 yara ne.
A hirarsu da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, shugaban hukumar kula da lafiya, matakin farko a jihar Filato, Dakta Livinus Miapkwap, ya ce manufar allurar rigakafin shi ne ta kare yara daga kamuwa da cutar ta sankarau.
Shi ma a na shi bayanin, Sakataran ma’aikatar lafiya ta jihar Filato, Dakta Martins Azzuwut, ya ce Najeriya na daga shiyyar da al’ummarta ke kamuwa da cutar sankarau, don haka ake neman mafita kan cutar.
Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Facebook Forum