Shugaban Hukumar Zikirullahi Olakunle Hassan ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja.
Wakiliyar Sashin Hausa Medina Dauda ta halarci taron, kuma ta aiko mana cewa, Shugaban Hukumar Alhazai Barista Zikirullah Olakunle Hassan ya ce hukumar za ta fara karbar Kudin maniyyata aikin Hajjin shekarar 2021 daga ranar 9 ga watan Satumba.
Ahaji Hassan ya kara da cewa hukumar, za ta bude wani sabon shafi na yanar gizo domin saukaka wa maniyyata rajista.
A lokacin da yake karin haske akan batun ko wasu maniyyata da ba su samu tafiya aikin hajjin bana ba za su kar6i kudadensu, Shugaban Hukumar Alhazan ya shawarci maniyyata aikin hajjin na badi da su fara tanadin kudadensu tun yanzu domin yin adashin gata a asusun hukumar.
Wani abinda ya dauki hankali shi ne yadda cutar coronavirus ta sa kasar Saudi Arabiyya ta soke aikin hajjin bana, sannan kuma ta yi karin kudaden haraji a kasar ta Saudiyya, to ko wanan kari zai shafi kudaden da Alhazai za su biya ?
Sai Kwamishina a Hukumar Alhazan Nura Ahmed Yakasai ya ce, “Abu guda daya da ya tabbata shi ne kasar Saudiyya ta yi kari ne akan haraji kawai, bayan shi abubuwa kaman makwanci da motocin sufuri ba a tabbatar da karin ba tukuna, tunda kowace shekara irin wadannan suna canjawa saboda haka burin hukumar shine a samu sauki saboda duk maniyyaci daga Najeriya ya samu halartar aikin Hajji.”
Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin nasarar da za a samu wajen gano maganin cutar coronavrus ko na rigakafinta saboda maniyyata su samu damar yin aikin hajjin.
A saurari cikakken rahotan Medina Dauda:
Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina
Facebook Forum