Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPC Ya Samu Ribar Naira Biliyan 674: Mele Kyari


Malam Mele Kyari
Malam Mele Kyari

A kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na ganin ta kara hanyoyin samun karin kudaden shiga a kasar, kamfanin man fetur na NNPC wanda a yanzu ke karkashin kulawar ma’aiktar kudi, ya sanar da samun gagarumar riba.

ABUJA, NIGERIA - A cewar kamfanin an samu riba Naira biliyan 674 a shekarar kasuwanci ta 2021 zuwa shekarar 2022, baya ga biyan haraji da ya zarce ribarsa ta biliyan N287 a shekarar 2020 da kaso 134.8 cikin 100.

Shugaban kamfanin NNPLC Malam Mele Kolo Kyari, ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata kamfanin ya samu gaggarumin bunkasa ta bangaren ribar kasuwanci, ya kuma ta'allaka nasarar da aka samu kan sabbin sauye-sauyen da suka aiwatar a kamfanin, da suka hada da inganta hulda da abokan kasuwanci, da kuma kara sanya ido kan yadda lamura ke gudana a kamfanin.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

A cewar kamfanin na NNPLC, masu satar danyen mai na janyo asarar gangar danyen mai dubu 200 a kullum, wanda ya rage ribar da ya kamata a samu a shekarar 2021 da ya kamata ta zarce abun da aka samu.

A bangaren iskar gas kuma shugaban ya yi karin haske kan inda aka kwana a shirye-shiryen gwamnatin Najeriya na fara fitar da albarkatun iskar gas zuwa kasashen turai la’akari da yakin dake faruwa tsakanin kasar rasha da Ukraine wanda hakan ya baiwa kasar damar cin moriya a kasuwar iskar gas ta duniya baki daya.

Malam Mele Kyari ya bayyana matakai da tsare-tsaren da za’a bi wajen cin gajiyar wannan aiki na Samar da Iskar gas.

“Na farko akwai tsarin da muke da shi da ake kira NNLG wato kamfanin da muke da jari a ciki kuma shi ne mafi girman hanyar saka gas a kasuwar duniya da ake kan shirin yi duk da cewa ba za mu ce za’a karasa shi yau ko gobe ba, amma muna sa ran cikin shekara uku za’a kammala shi kuma za’a ga amfanin shi cikin kasuwa," in ji Mele Kyari.

Wata rijiyar hakar mai da iskar Gas daga karkashin ruwa.
Wata rijiyar hakar mai da iskar Gas daga karkashin ruwa.

Kwararre a harkan man fetur da iskar gas a Najeriya, Muhammad Saleh Hassan, ya ce kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi wajen shigo da kamfanoni da masu hannu da shuni a bangaren saka hannayen jari a fannin iskar gas, ya yi nuni da cewa za’a sami nasara a wannan fannin.

Najeriya dai ta kasance kasa mafi girma da ke samar da iskar gas a Afirka kuma ta 10 a duniya inda take da kadada biliyan 209.5 na iskar gas kana take iya samar da iskar gas mai cubic biliyan 8 a kowace rana a cewar hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta kasar.

Kuma tuni Gwamnati dai ta bayyana cewa za ta gina bututun iskar gas na Najeriya tare da hadin gwiwar kasar Aljeriya inda daga nan za’a rinka kai wa kasashen Turai, aikin da ake ganin zai ci sama da dala biliyan 10 an kuma bude kofa ga kamfanoni da ke da sha’awar zuba hannayen jari a bangaren.

Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

NNPC Ya Samu Ribar Naira Biliyan 674: Mele Kyari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG