Gwamnatin jihar Kaduna ta soma kwato wasu filaye da tace mallakar gwamnati ne.
Kwana biyar da fara rushe gidaje kan filayen da gwamnati tace nata ne wasu da abun ya shafa sun soma korafi.
A yankin Zaria inda gwamnati ta fara rushe gidaje wasu da lamarin ya shafa biyo bayan ruguje gidajensu sun shiga halin rudani.
An fara rushe-rushen ne a makarantar Al Huda Huda dake garin Zaria wurin da wasu suka gina gidaje kan filayen dake harabar makarantar.
Murtanen sun koka suna cewa suna neman doki. Wata da take magana da kuka tace gidajensu biyu aka rushe kuma shekaru ishirin ke nan da suka sayi wurin. Mijinsu mutumin Zamfara ne amma mazaunin Zaria.
Malam Yusuf Kadi ya ce sun yi bakin ciki da abun da ya faru dasu. Abun bakin cikin shi ne an basu wa'adin kwanaki 21 su tara nasu-inasu su fice. Amma sai gashi yawancinsu basu da inda zasu ko kuma abun da zasu ci. Wasu suna cikin tara kayansu sai ga jami'an tsaro sun zo suka koresu kana suka soma ruguje gidajen. Akwai wani ma da mata uku da 'ya'ya 25 . Sun nemi gidan haya basu samu ba soboda yawansu.
Amma duk da hakan akwai wasu mazauna cikin birnin Zaria dake goyon bayan shirin na gwamnatin jihar.
Wani mazaunin Zaria yace ainihi can an bada filayen ne domin a noma kuma duk wata takarda da aka bayar ta wucingadi ce. Saleh Kasidi yace wadanda suka shiga cikin makaranta suka yi gini basu kyauta ba.
Mr Samuel Aruwan mai magana da yawun gwamnatin jihar ya bayyana cewa aikin da gwamnati take yi ba wai tana duban fuskar mutum ba ne ko addini ko kabila ko jinsi. Tana yi ne tsakaninta da Allah da nufin ceto kaddarorin al'ummar jihar.
Kafin gwamnati ta dauki matakin da ta dauka sai da ta kafa kwamiti tayi nazari akan maganar ta kuma bada sanarwa. Akwai mutanen da suka kwashe kayansu cikin mako daya suka mikawa gwamnati filayenta da kaddarorinta..
A wanna makon fafutikar kwato filayen da wasu kaddarorin gwamnati zai cigaba a birnin Kaduna da ma wasu wuraren.
Ga rahoton Lawal Isa Ikara.