A wani sako da ta aika wajen taron, ministar kudin Najeriya Mrs. Kemi Adeosun, ta ce makasudin taron shi ne tattaunawa da kuma gano hanyoyin da za a samu kudaden shiga domin gudanar da ayyukan ci gaban al’umma, ta yadda za a kaucewa basuka da ke tattare da makudan kudin ruwa.
Daraktan ma’aikatar kudi ta Najeriya, Alhaji Aliyu Ahmed, wanda shi ne ya wakilci ministar kudi a taron, ya ce gwamnati ta mayar da hankali ne wajen samo kudade daga bankunan Musulunci domin kaucewa tsadar biyan kudun ruwa.
Wannan wata hanya ce da bankunan Musulunci za su sami damar cudanya da sauran bankunan kasashen Musulmi na duniya don samar da ci gaba ga al’umma, a cewar Alhaji Garba Imam, shugaban wani kamafani da ke hada-hadar kudade na islama dake Abuja.
Yanzu haka dai Najeriya ta na da bankin Islama guda daya da ake kira Ja’iz Bank, wanda ya sami lasisin gudanar da harkokin kudi tun shekarar 2016.
Haka kuma bincike na nuni da cewa akwai cibiyoyin kudi har 50 a sassa na Duniya.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum