Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Zata Binciki 'yan Sanda Kan Batun Dino Melaye


Dino Melaye
Dino Melaye

Majalisar datijjan Najeriya ta umurci kwamitinta ta shari’a a yau Talata da ta binciki gayyatar da hukumar ‘yan sanda ta yi wa Senata Dino Melaye a cikin sa'o'i 48.

An cimma matsayar ne bayan wani kudiri da Senata Hamman Misau mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya kawo, na cewa ‘yan sanda na saka son zuciya akan gayyatar Senata Dino Melaye, har suna barazanar bayar da sammacen kama shi.

Senatan ya bayyana cewa “ina kira ga majalisa da ta dubi abinda ke faruwa a jihar Kogi. Zaku iya tuna jami’in yada labaran ‘yan sanda Jimoh Moshood ya gabatar da wadansu masu laifi inda ya bayyana a wani taron manema labarai cewa Senata Dino Melaye ne ya sayo musu makamai kuma ya basu zunzurutun kudi har Naira dubu 430.” A cikin takaici ya kara da cewa wadannan masu laifiin sune kuma wadanda aka kama a baya akan yunkurin kashe shi Dino Melaye din.

Senata Philip Aduda ya kara da cewa gwamna Yahaya Bello babbar barazana ne ga dimokaradiyya inda yace dole a taka mishi birki.

An bar Gwamnan Jihar Kogi ya yi duk abin da yake so kuma idan ba a kula da shi ba, wannan mulkin demokradiyya zai kauce."

"Ace wanda ya sami goyon baya mafi girma ya fara zama irin wannan abu, kuma ya zama abin da ya zama. Ina ganin dole ne a yi wani abu a kai. "

Sanata Biodun Olujimi ya jaddada cewa, majalisar tana da girma da zata iya yanke shawara, inda ya ce dole ne Yahaya Bello ya dubi abin da ke faruwa a jihar.

Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya yi mamakin cewa: "Idan aka kama wadanda sukai yunkurin kashe gillar Dino Melaye kuma ace shine yake siya musu makamai? Akwai ayar tambaya abatun

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG