Majalisar Dattawa ta amince da dokar da za ta baiwa yan kasa damar yin kwarmato ko yekuwa idan sun gano kudade da aka tabbatar cewa na sata ne.
An dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa kan batun dokar da zata karfafa yekuwar yaki da cin hanci da rashawa, ko sama da fadi da dukiyar al’umma. Dokar na ‘dauke da sharuda masu yawa da suka hada da wadda zata kare wanda yayi yekuwa akan kudaden da aka tabbatar na sata ne, da kuma sharudan da zasu bayar da damar ‘daure mutum idan yayi kwarmato kan ‘karya.
Da yake ‘karin haske kan dokar Sanata Shehu Sani, yace dokace da zata karfafa ‘yan ‘kasa karfin gwiwar fitowa su sanar da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa wasu ayyuka da suka shafi boye kudade da sace-sace da yiwa kasa zamba.
Haka kuma dokar ta kare jama’a kan kazafi da karya da kuma cin mutunci, kasancewar mutane zasu iya amfani da damar wajen yiwa wasu da basa ‘kauna sharri. Dokar dai ta bayyana karara cewa idan mutum ya bayyana gaskiya aka samo kudin mutum zai sami kasonsa, idan kuma aka tabbatar da cewa mutum ya yi karya, hukuncin dauri ne a gidan kaso.
Sanata Binta Masi Garba, ta ce Majalisa ta yi dokar ne domin inganta yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Tun hawan gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari, ake fara yaki da cin hanci da rashawa na ba sani-ba-sabo, don kama duk wani ko wata jam’an gwamnati da suka sace dokiyoyin al’umma, tare da hukuntasu.
Domin karin bayani saurari rahotan Madina Dauda.
Facebook Forum