Mawakin dai ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci wasu sansanonin ‘yan gudun hijira a garin Maiduguri. Inda yake shirin shirya wasa na Musammam da zai kwantar da hankulan ‘yan gudun hijirar da ke tsugunne a irin wadannan sansanoni.
Mawakin yace wadannan ‘yan gudun hijirar suna cikin halin kaka ni kayi, domin sabo da irin yadda yaje ya gansu da irin halin da suka shiga, wanda yace akwai bukatar gwamnati ta matso don tallafawa wadannan ‘yan gudun hijirar da yanzu hakan suke neman bukatar taimakon gaggawa daga dukkanin al’ummar Nageria.
‘’Yace yawan wadannasn kauyuka da garuruwa da muke dasu,ba wani lokaci da gwamnati ke kaiwa gare su sai lokacin zabe kawai kuma wasun su suna cikin jahilci sai su amsa domin basu san illar karban wannan kyautar ba, shi yasa wata kungiya zata iya zuwa ta rude su da wani abin hannu nan da nan sai kaga ansha karfin su, ana irin haka a sassan duniya daban-daban’’
Ga Haruna Dauda Biu da Karin bayani
Facebook Forum