A wajen wani taro da aka shirya domin fadakar da al’ummar wasu jihohi na yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya a birnin Ilori na jihar Kwara, ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed, yayi watsi da kalaman wasu shugabannin addini da kuma wasu kalaman da suke fitowa daga kasashen ketare, wanda ke nuna ana zaluntar al’ummar Krista a tarayyar Najeriya.
Ministan yayi zargin cewa a kwanan nan kafofin yada labarai sun cika da kalamai da ke nuna cewa ana zaluntar Kristoci abin da yace hakan ba zai haifarwa ‘kasar ‘da mai ido ba.
Ya ci gaba da cewa kalamai da ake cewa ana so a mayar da Najeriya kasar musulmai da kuma cin zarafi da cin zalin Kristoci, babu abin da zai harfar sai yaki na addini a ‘kasar.
A kwanan nan ne dai wani ‘dan Majalisar Wakilan kasar Amurka, wanda ke zama shugaban kwamitin kula da Lafiya da kuma ‘yancin bil Adama Christopher Smith, ya bayyana irin kalubalen da yace Kristoci na fuskanta a Najeriya. ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa ya sha ziyartar Najeriya, inda yake ganewa kansa yadda zamantakewa take tsakanin Krista da Musulmai.
Ministan yada labaran Najeriya, yayi kira ga mabiya addinin Krista da kuma Musulmai da suyi koyi da jagoranci irin na mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na Uku da kuma Cardinal Onaiyekan na Cocin Katolika na Abuja, dangane da kungiyoyin da suka kafa na sasanta al’ummar Musulmai da Krista.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.