A irin wannan tashin hankalin ne wurin hakan ma'adanai ya sa rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta cafke wasu mutane biyar da ake zarginsu da hannu a kisan wasu mutane fiye da goma a wurin hakan ma'adanai a kauyen Gyero dake karamar hukumar Jos ta Kudu.
Lamarin ya auku ne a makon da ya gabata bayan da musu ya barke tsakanin masu hakan kuzan a yankin Gyero. Lamarin ya kaiga tashin hankali da rasa rayukan mutane tare da kona gidaje da dama.
Kwamandan rundunar Manjo Janar Nicholas Rogers yace baicin cafke mutanen sun kuma kama bindigogi kirar AK-47 guda 47 da albarusai da bindiga mai sarafa kanta da dai sauran makamai masu hadarin gaske.
Kwamanda Rogers yace ko a lokacin da ya isa wurin mutanen suna kan fada. Ya gargadi matasa da su guji daukan doka a hannunsu. Ya kuma bukaci shugabannin al'umma da su dinga sanar da jami'an tsaro a duk lokacin da aka samu masu tada hankali.
Gwamnan jihar ya yabawa jami'an tsaro wajen kiyaye tashin hankali tsakanin masu hakan kuza a jihar. Kana gwamnan yace duk masu hakar ma'adanai ba bisa kan ka'ida ba to su kuka da kansu inda aka kamasu.
Ga Zainab Babaji da karin bayani.