Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola: Yajin Aikin Ma'aikatan Lafiya Na Barazana Ga Aikin Tantance Matafiya a Najeriya


Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yi wa Mahajjata gwajin cutar Ebola
Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yi wa Mahajjata gwajin cutar Ebola

Umurnin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar na a fara tantance matafiya daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da cutar Ebola ta bulla ka iya fuskantar tsaiko yayin da ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya ke ci gaba da yajin aiki, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya sun dukufa wajen dakile yaduwar cutar Ebola wacce ta sake bulla a kasar.

A karshen makon nan ne, bangarorin biyu suka maida hankali wajen aikawa da kwararrun zuwa sassan da aka samu asarar rayuka 30 sanadiyar bullar cutar a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hakan kuma na faruwa ne a daidai lokacin da hukumomin Najeriya suka ba da umurni ga ma'aikatan kiwon lafiya da su tabbata an gudanar da gwaji tantancewa ga duk wani matafiyi da ya fito daga kasar ta Congo da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

Sai dai bayanan da jaridun Najeriyar ke wallafawa na nuni da cewa wannan umurni ka iya fuskantar matsala, domin ma'aikatan kiwon lafiyan kasar na yajin aiki.

Wani bincike da jaridar Punch ta gudanar ta kuma wallafa a shafinta na yanara gizo, ya gano cewa, babu duriyar ma'aikatan kiwon lafiyar a filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke Legas a kudu maso gabashin kasar.

Ma'aikatan kiwon lafiya da suka hada da masu kula da marasa lafiya da masu gwaje-gwajen cututtuka da sauran masu tallafawa likitoci sun tsunduma cikin yajin aiki tun a ranar 18 ga watan Afrilu.

Kukansu shi ne, suna neman a kara masu kudaden albashi daidai da na likitoci.

Hakan kuma a cewar masu lura da al'amura ka iya zama barazana ga lafiyar matafiya da ma kasar baki daya.

A tsakanin shekarar 2014 barkewar cutar ta Ebola a kasashen Saliyo da Congo da wasu kasashen yankin, ta yi sanadiyar shigar cutar mai saurin kisa cikin Najeriya, inda mutum bakwai cikin 19 suka rasu.

Najeriya ba ta hada kan iyaka da duk wadannan kasashen ba amma sanadiyar tafiye-tafiye cutar ta bulla a kasar.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG