Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Ta Sake Bulla a Kasar Kongo (Congo)


Masu yaki da cutar Ebola
Masu yaki da cutar Ebola

Yayin da aka fara mancewa da cutar Ebola, sai kawai cutar ta sake bulla a kasar Kongo, inda ta hallaka mutane akalla 17 baya ga galabaitar da wasu da ta yi. Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya ta fara daukar mataki.

Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bayyana sake bullar cutar Ebola a yankinta na Bikoro da ke lardin Equateur, bayan da mutane 17 su ka mutu daga cutar da ake kyautata zaton Ebolar ce, aka kuma tabbatar da cutar jikin wasu mutane biyu.

Ita ma Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta sanar jiya Talata cewa kasar ta Congo na fama da wata sabuwar bullar cutar ta Ebola, sannan ta ce tuni ta fitar da dala miliyan guda daga asusunta na gaggawa don taimakawa wajen yakar cutar.

Hukumar ta WHO ta ce cikin makonni biyu da su ka gabata, an samu wasu mutane 21 da ake kyautata zaton suna dauke da wani nau’in zazzibi mai alaka da Ebola a yankin. Mutane 17 din sun mutu ne sanadiyyar wannan zazzabin.

A 2017 aka yi fama da bullar cutar Ebola ta karshe a yankin Likati da aka kebe don ayyukan jinya, inda hudu daga cikin mutane 8 da su ka kamu da cutar su ka mutu. Wannan ne karo na 9 na bullar cutar ta Ebola tun bayan da aka gano cutar a 1976, aka kuma sa mata sunan wani kogin yankin wato Ebola.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG