A baya mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ziyarci jihohin Delta da Bayelsa.
An dai gabatar da jawabai da dama wadanda suka nuna da Gwamnatin tarayyar Najeriya, bisa halin da aka bar yankin Niger Delta, na mayar da shi saniyar ware.
Daga cikin masu jawabai har da ‘yar jihar Madam Ankiu, wacce ta ce abinda ya fi damun su ‘yan yankin Niger Delta, shi ne na kula da hakkokinsu domin tabbatar da adalci a harkokin yankin na Niger Delta.
Shi kuwa Gwamnan jihar ta Rivers Barrister Ezenwo Nyesom Wike, ya ce babu tababa yakin Niger Delta, na fama da kalubale masu yawa kuma arzikin yankin ne ke rike da Najeriya tsawon shekaru hamsin da suka gabata kuma Gwamnatocin da suka shude sun bar yankin a wulakance.
A na shi jawabin mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ziyarar tawagar na bayyanawa al’umar yankin irin tanadin da gwamnatin tarayyar Najeriya, ta yiwa yankin na Niger Delta, ne da kuma batun tabbatar kwanciyar hankali a yankin.