WASHINGTON DC —
Wannan gagarumin farmakin da sojojin saman Najeriyar za su fara kaddamarwa da manyan jiragen yaki an yi mai taken 'Operation Dirar Mikiya'.
"Wannan wani farmaki ne ta sama domin fatattakar 'yan bindiga daga Jihar Zamfara da kuma yankunan ta," in ji Babban kwamandan rundunar sojin kundunbala na mayakan saman, Air Vice Marshall Akpasa Samson Okon, wanda shi da kansa ke jagorantar wannan farmaki.
Ya bayyana cewa rundunar ba ta da inda manyan jiragen yaki za su rika sauka ko tashi daga Gusau. Yanzu ana amfani da filin jirgin saman Katsina a cewarsa, don haka ne aka jibge jirage masu yawa a can sannan wasu da yawa na nan tafe har da kuma dakaru na musamman su ma na bisa hanya da kayan aiki.
Ya ci gaba da cewa wannan wani mataki ne na a-yi-ta-ta-kare, da suke son kaddamarwa. A don haka ne rundunar ta kawo kayayyakin yaki da suka hada da manya-manyan jiragen yakin sama.
"Ya kamata a ce an dauki wannan mataki tuntuni, " inji wani tsohon sojan sama, Air Kwamanda Ahmad Tijjani Baba Gamawa, saboda yadda abubuwa suka yi tsamari a jihar Zamfaran.
Sai dai wani kwararre ta fuskar tsaro Mallam Kabiru Adamu, ya ce duk wani yunkurin da za a yi wanda bai hada da mamaye dazuzzukan dake yankin ba, domin dakile damar canza wuri daga wannan dajin zuwa wancan ba - kamar yadda zafin wuta ya koro 'yan bindigan zuwa Birnin Gwari, sannan kuma tsakanin kasashe da ke makwabtaka da nan wato Nijar kenan, to da wuya ya yi tasiri.
Saurari cikakken rohoton
Facebook Forum