Tashin bam din na farko ya farune a dai dai lokacin da ake haramar yin sallar Asuba a wani masallaci dake unguwar ma’aikatan jami’ar dake cikin makarantar, lokacin da ‘yar kunar bakin waken ta tayar da bam din jikinta kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutanen uku, ciki harda wani Farfesa na jami’ar.
Yayin da wadda ke dauke da bam din na biyu, wadda ta tsallaka ta Katanga ta shiga jami’ar, inda jami’an dake tsaron jami’ar suka yi kokarin tsayar da ita nan take ta tayar da bam din jikinta ta kashe kanta ba tare da ta kashe kowa ba, sai dai ta lalata wasu motoci dake kusa da ita.
A dadin mutane biyar ne suka rasa rayukansu ciki har da su ‘yan kunar bakin waken guda biyu, sai kuma mutane 15 da suka raunata kuma suke karbar magani a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Wakilin Muryar Amurka dake Maiduguri, Haruna Dauda, ya ziyarci masallacin da aka kai harin inda ya ganewa idanunsa rugujewar gini har saman rufin masallacin ya tashi, babu wani abu sai baraguzai da zubewar jinin mutanen da harin ya rutsa da su.
Mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri, Farfesa Abubakar Jodi, ya tabbatar da afkuwar lamarin wanda kuma ya shaidawa gwamnan jihar Borno cewa yanzu haka an dakatar da jarabawar da a halin yanzu ke gudana a jami’ar.
Wannan dai shine karo na farko da aka taba samu irin wannan tashin bam din a cikin jami’ar Maiduguri.
Domin Karin Bayani.