Mambobin kwamitin bunkasa tattalin arziki na ECOWAS sun taru a hedkwarar ECOWAS din dake Abuja domin tattauna lamuran bunkasa noma da kiwo a yankin Afirka ta Yamma da kuma kawo karshen duk wata fitina tasakanin manoma da makiyaya.
Dr Aliyu Ibrahim na kwamitin raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ko ECOWAS dake kula da harkokin bunkasa noma da kiwo a taron hanyar zayyana kawo karshen fitina tsakanin makiyaya da manoma da hakan kan kaiga hasarar rayuka da dukiyoyi yace zasu rubuta littafi.
Littafin zai zayyana yadda noma da kiwo zasu bunkasa a tsawon shekaru goma nan gaba. Dr Ibrahim yace ta bangaren manoma da makiyaya wasu ne masu ilimin zamanin dake birane suke zugasu saboda babu yadda za'a yi manoma su rabu da makiyaya. Yace zasu cigaba da fada masu cewa su Danjuma ne da Dan Jummai.
Sarkin Fulanin Augie Abubakar Aliyu Kirwa yace dagewa ta hanyar kafa gandun kiwon shanu zai kawo masalaha yana kuma mai cewa babu wata ribar da sassan biyu zasu samu da yin rigima da juna. Tashintsahina tsakaninsu ma kan budewa 'yan ta'ada hanyar shigowa su hallaka makiyayan.
Inji Abubakar Aliyu Kirwa babu yadda makiyayi zai yi dole ne ya tashi ya nemar masu abun da zasu ci.
Makiyayin zamani Yariman Muri ya bada shawarar samar ma makiyaya harawa da sakawa manoma. Ya lissafi ciyawa iri iri da za'a iya shugakawa da ya kamata a raya makiyaya su daina yawo. Idan an kebewa Fulani daji to yaransu zasu zama masu shan giya kana satar shanu zai karu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.