Fiye da mutane dubu dari bakwai ne suka yi jerin gwanon tsit a biranen kasar Faransa jiya Asabar domin nuna goyon baya wa mutane goma sha bakwai, da tarzoma mafi muni da kasar ta gani, cikin fiye da shekaru da hamsin ta rutsa dasu.
Haka kuma a yau Lahadi miliyoyin mutane ciki harda shugabanin kasashe ne ake sa ran zasu yi jerin gwano a birnin Paris domin nuna goyon baya ta yan uwantaka ga Faransawa.
An shirya Prime Ministan Britaniya David Cameron da shugabar Jamus Angela Merkel da Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas zasu halarci gangamin.
Za'a ci gaba da daukan tsauraran matakan tsaro a yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma farautar budurawa daga cikin 'yan ta'ada uku da aka kashe a ranar Juma'a.
Jami'an tsaro sun dukufa wajen neman Hayat yar shekara ashirin da shidda da haihuwa, wadda da farko anyi tsamanin ta arce a lokacin hayaniyar kutsawar da yan sanda suka yi kasuwa a yunkurin kubutar da wadanda aka yi garkuwa dasu.
Fiye da mutane dubu dari bakwai ne suka yi jerin gwanon tsit a biranen kasar Faransa jiya Asabar, domin juyayin mutane goma sha bakwai da aka kashe.