Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 26 Sun Mutu Sanadiyyar Harin Kunar Bakin Wake A Kabul


Britain's Prince Charles, center, and Prime Minister Boris Johnson, right, shelter from rain during the unveiling of the UK Police Memorial at the National Memorial Arboretum at Alrewas, England.
Britain's Prince Charles, center, and Prime Minister Boris Johnson, right, shelter from rain during the unveiling of the UK Police Memorial at the National Memorial Arboretum at Alrewas, England.

A wata sanarwa da aka fitar, Muryar Amurka ta bayyana bakin cikinta game da mutuwar wasu 'yan jarida na gidan radiyon RFE a birnin Kabul.

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 26, ciki har da ‘yan jarida 9. Wasu su 50 kuma sun jikkata, ciki har da ‘yan jarida 5.

Kungiyar ISIS, ta kamfanin dillancin labaranta, ta dauki alhakin kai harin, mafi muni da aka taba gani akan ‘yan jarida a Afghanistan.

Hukumar da ke sa ido akan ‘yan jarida a Afghanistan da ake kira AJSC a takaice, a yayin da ta ke tabbatar da mummunan harin da ya shafi ‘yan jarida, ta yi Allah wadai da harin da kakkausan lafazi.

Wasu mata biyu ‘yan jarida, ciki har da Maharram Durrani daga RFE/RL, na daga cikin wadanda su ka mutu. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya tabbatar da mutuwar babban mai daukar masu hotuna a Kabul, Shah Marai. Wasu ma’aikatan RFE guda biyu, Abdullah Hananzai da Abawoon Kakar, na cikin wadanda suka mutu.

Hukumomin Afghanistan da wadanda su ka shaida lamarin sun ce an fara harin ne da sassafe, yayinda mutane ke yawan zirga-zirga, a lokacin ne wani dan kunar bakin wake akan babur ya tada nakiyarsa a kusa da ofishin leken asirin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG