Wakilan tawagar Majalisar Dinkin Duniya, MDD dake binciken take hakkokin bil adama a Myammar sun gana da shugaban kasar Aung San Suu Kyi, biyo bayan ziyarar da suka kai a Bangladesh, inda yan gudun hijira dubu dari bakwai da suka arcewa tashin hankali a jihar Rakhine na Myanmar ke zaune.
A jiya Litinin tawagar kwamitin sulhun MDD mai wakilai 15 ta gana da Aung San Suu Kyi da kwamandan sojoji Senior General Min Aung Hlaing a birnin Naypyitaw.
A yau Talata ne tagawar zata je jihar Rakhine inda ake tashin hankali, domin ta ga abin da ke faruwa bayan matakan murkushe mazauna yankin da sojoji suka fara tun cikin watan Agustan bara, kana su ga irin shirin da kasar take yi ta dawo da yan gudun hijira da galibinsu yan kabilar Rohingya marasa rinjayi ne.
An ki baiwa yan Rohingya yancin zama yan kasa, duk da cewar yawancin iyalansu sun zauna Myammar karnoni da dama. 'Yan gudun hijirar sun tserewa tarzomar da ake yi ne a jahar Rakhine, lamarin da MDD ta kira bisa dukkan alamu kisan kiyashi ne.
Facebook Forum