Wani jirgin yaki mai saukar ungulu da ke dauke da wasu jami’an gwamnatin Mexico ya fadi jiya Jumma’a a yayin da su ke dudduba irin barnar da girgizar kasar da ta auku ta yi. Jirgin ya kashe wasu mutane biyu da ke kasa.
Jirgin na dauke ne da Ministan Cikin Gidan Mexico Alfonso Navarrete Prida da kuma gwamnan jahar Oaxaca Alejandro Murat, wadanda ba su ji wani mummunan rauni ba.
Girgizar kasar ta auku ne a Kudancin Mexico jiya Jumma’a, inda ta yi wata ‘yar barna a jahar Oaxaca, to amma nan take babu wani rahoton mutuwa ko jin rauni.
Cibiyar binciken karkshin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar na da karfin 7.2 a ma’aunin girgizar kasa kuma ta samo asali ne a wani yankin karkara na kudancin jahar ta Oaxaca daura da gabar Tekun Pacific da kuma kan iyakar jahar Guerrero.
Facebook Forum