A cikin takardar tuhumar da masu taimakawa gwamnatin tarayya tantance laifi suka bayar, an yi zargin cewa, wani kamfanin nazarin hanyar sadarwar internet dake da cibiya a Rasha, wanda kuma yake da alaka da Kremlin, da ma'aikatansa goma sha biyu sun gudanar da wadansu ayyuka da nufin yin katsalandan a zabe, da kuma tsarin siyasar Amurka daga shekara ta dubu da dari biyu da goma sha hudu zuwa zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida.
An hakikanta cewa, kamfanin ya taka muhimmiyar rawa a katsalandan din da ake zargin Rasha da shi a zaben shugaban kasa, ta wajen yin aiki da shafunan sadarwa na boge, da biyan masu amfani da hanyar sadarwar internet da wadansu hanyoyi da nufin karkata sakamakon zaben don shugaba Donald Trump ya sami galaba.
An kuma tuhumi mai daukar nauyin cibiyar nazarin ta hanyar internet, wani dan kasuwar kasar Rasha Yevgeniy Prigozhin, da wadansu kamfanoni biyu dake karkashin ikonsa,Concord Management da Consulting and Concord Catering. Takardar tuhumar ta bayyana cewa, Prigozhin da cibiyoyin kasuwancinsa. sun bada makudan kudi ga kamfanin nazarin hanyar sadarwar internet da nufin yin katsalandan a zaben da aka gudanar a Amurka cikin shekara ta dubu biyu da goma sha shida.
Facebook Forum