Musulmi zasu yi dawafi suna kewaye Ka'aba, ginin da musulmi ko a ina a duniya suke fuskanta lokacinda suke sallah.
Hajji na daya daga cikin cikakan musulunci idan musulmi yana da hali akalla sau daya a rayuwarsa. Saura cikakan sun hada da imani da kadaicin Allah da Annabi Muhammadu a zaman manzo na karshe, da fidda zakka da kuma azumi cikin watan Ramadan da sallah lokaci biyar kowace rana.
Ga musulmi masu yawan zuwa hajji yana daga muhimman nasarori a rayuwarsu.
Hadarin kugiyar daukar kayan gine gine da ya auku a farkon watan nan a Ka'aba har mutane 109 suka halaka bai sa mahajatta sunyi kasa a guiwa ba.
Akalla wasu 400 suka jikkata.
A arfan ne Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yayi hudubarsa ta karshe shekaru dubu daya da dari hudu da suka wuce.